Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Netherlands Zasu Yi Aiki Tare Don Hukumta 'Yan Fashi Cikin Teku


Amurka da kasar Netherlands sun lashi takobin yin aiki tare don yin shari'ar 'yan fashi cikin teku da suka addabi jiragen ruwa a dab da gabar kasar Somaliya. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta fada jiya litinin cewa kasashen biyu sun yarda zasu tattauna da kungiyar NATO kan hanyar da ta fi dacewa ta gurfanar da 'yan fashin gaban shari'a a bayan an kama su.

Clinton ta yi wannan furuci ne tare da ministan harkokin wajen Netherlands, Maxime Verhagen, wanda yake ziyara a nan Washington.

A ranar lahadi sojojin NATO suka murkushe wani farmakin da Somaliyawa 'yan fashi suka kai kan wani jirgin ruwan kasar Norway. Wani jirgin ruwan mayakan Canada ya kama 'yan fashi 7, amma sai aka sake su saboda rashin wata madafar shari'a ta rike su.

Clinton ta ce sakin 'yan fashin ba shi ne abinda ya dace ba. Ta ce a cikin watan Mayu mai zuwa kungiyar tuntubar juna kan yaki da fashi cikin teku zata gana a New York don tattauna wannan batun.

XS
SM
MD
LG