Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sri Lanka Ta Umurci 'Yan Tawayen Tamil Tigers Da Su Ajiye Makamai Su Mika Kai Nan Da Tsakar Rana Yau Talata


Gwamnatin Sri Lanka ta bada 'yan tawayen Tamil Tigers wa'adin sa'o'i 24 da su mika kawunansu, a bayan da sojoji suka kwato dubban fararen hula daga sauran yanki kwaya daya tak da ya rage a hannun 'yan tawayen.

Kakakin ma'aikatar tsaron Sri Lanka, Keheliya Rambukwella, ya fadawa Muryar Amurka jiya litinin cewa tilas ne madugun 'yan Tamil, Velupillai Prabhakaran, da dakarunsa su ajiye makamai nan da karfe 12n rana agogon Sri Lanka, watau karfe 7 da rabi na safiyar nan agogon Nijeriya, ko kuma a far musu.

Wannan gargadin ya biyo bayan fasa wani shingen da 'yan tawaye suka kafa da sojojin gwamnati suka yi, suka kwato fararen hula dubu 35 da aka rutsa su a cikin yankin da ya rage a hannun 'yan tawaye.

XS
SM
MD
LG