Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako 'Yar Kasar Canada Da Aka Sace A Kaduna


An sako wata mace 'yar kasar Canada da aka sace a farkon wannan wata a Nijeriya, an kuma mika ta ga jami'an kasar Canada.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Canada ya fada a birnin Ottawa cewa a yanzu Julie Mulligan "tana nan lafiyarta kalau, kuma tana hannun jami'an Canada." A cikin wata sanarwar da ya bayar larabar nan, kakakin ya ce ana kyautata zaton nan ba da jimawa ba Mulligan zata yi ido hudu da iyalanta.

A ranar 16 ga watan Afrilu wasu 'yan bindiga suka sace Mulligan a birnin Kaduna dake arewacin Nijeriya. Kwanaki da dama a bayan wannan, mutanen ad suka sace ta sun yi ikirarin cewa ba ta da lafiya sosai, tana fama da zazzabin cizon sauro da kuma kuraje.

Da farko, 'yan sandan Nijeriya sun ce mutanen da suka sace Mulligan sun nemi da a biya su kudin fansa. Amma kuma ba a ji labarin ko an biya su kudin fansar ba.

Sace mutane ad wasu hare-hare sun zamo ruwan dare a yankin Niger Delta na kudancin Nijeriya, amma ba a saba ganin irin wannan a sauran sassan Nijeriya ba.

XS
SM
MD
LG