Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gurfanar Da Nasiru el-Rufa'i A Gaban Kotu


An sake gurfanar da wani tsohon minista na tsohuwar gwamnatin Olusegun Obasanjo a gaban kotu a Nijeriya.

A jiya Laraba Hukumar Yaki da Laifuffukan Tattalin Arziki ta EFCC ta tuhumi Malam Nasir El Rufa'i, tsohon ministan babban birnin tarayya, Abuja, da laifuffuka takwas na hadin baki, da rashawa.

Masu bincike sun zargi Malam El Rufa'i da laifin yin amfani da matsayinsa, ya bayar da wani fili na Hukumar Samar da Wutar Lantarki, wanda ya saba wa dokokin kasa.

Ance Ministan Babban Birnin Taraiya na yanzu, ya fara soke takardun mallakar wasu filaye da Malam El Rufa'i ya bayar a karshen wa'adin aikinsa.

Shugaba Obasanjo dai yana shan zarge zargen rashawa, tare da wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin sa.

XS
SM
MD
LG