Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jacob Zuma Shi Ne Shugaban Afirka Ta Kudu Na Gaba


Majalisar dokokin Afirka ta Kudu, ta zabi shugaban Jam'iyyar ANC mai Mulki, Jacob Zuma, a matsayin shugaban kasar na gaba.

Masu goyon bayan Mr. Zuma 277 ne suka kada masa kuri'a, a majalisar wadda Jam'iyyar ANC ke da rinjaye, 47 kuma suka kada kuri'ar rashin amincewa, a kuri'un da aka kada a jiya Laraba.

Bayan an kada Kuri'ar, shugaban mai jiran gado yace babban abin da gwamnatinsa zata sa a gaba shine daukar kwararan matakan tunkarar matsalar tattalin arziki dake shafar duniya.

A jawabin da ya yiwa majalisar, Mr. Zuma yace gwamnatinsa zata dauki matakan habaka ilmi, da harkokin lafiya, da yaki da miyagun laifuffuka, da samarda aikin yi, da kuma gyara dokokin mallakar kasa. Ya kuma yi alkawarin kyautata dangantaka da jam'iyyun adawa.

Ranar Asabar za a yi bikin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, ranar lahadi kuma zai nada majalisarsa ta zartaswa.

XS
SM
MD
LG