Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Pakistan Ta Ce Dakarunta Sun Ceto Dalibai Kurata Da 'Yan Taliban Suka Sace


Rundunar sojojin Pakistan ta ce dakarunta sun ceto wasu daliban kuratan soja su kimanin 80 da ma’aikatan makarantarsu wadanda ‘yan tsageran Taliban suka sace jiya litinin a yankin arewa maso yammacin Pakistan.

Kakakin rundunar sojoji, Manjo-janar Athar Abbas, ya fada yau talatar nan cewa sojoji sun kwato wadannan dalibai kurata a lokacin da tsageran suke kokarin tsallakawa da su daga yankin Waziristan ta Arewa zuwa Waziristan ta Kudu.

Ba a san ko dalibai kurata nawa suka rage a hannun ‘yan tsageran da suka sace su jiya litinin ba, kuma har yanzu babu cikakken bayanin yadda ‘yan tsageran suka sace wadannan dalibai masu yawa. Tun fari, hukumomin Pakistan sun ce tsageran Taliban dauke da manyan makamai sun tsallaka gundumar Bunna jiya litinin daga cikin Waziristan ta Arewa, suka sace kuratan daliban soja masu yawa dake tafiya a cikin wata kwambar motoci.

An ce daliban sun fito ne daga wata makarantar horas da sojojin gwamnati ta maza da ake kira Razmak Cadet College a Waziristan ta Arewa.

Da farko hukumomin gundumar Bannu sun ce kwambar motocin tana dauke ne da mutane 400 wadanda suka hada da dalibai da malamai da kuma iyaye. Amma bayanan da aka samu daga bisani sun ce da yawa daga cikin mutanen dake tafiya cikin kwambar sun tsere, kuma yawan mutane da motocin dake tafiya cikin kwambar bai kai yawan da aka bayyana tun farko ba.

XS
SM
MD
LG