Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Komo Gida Daga Ghana


Shugaba Barack Obama ya komo gida Amurka a bayan ziyarar mako guda da ta kai shi Moscow a kasar Rasha, da taron kolin kasashen G-8 masu arzikin masana'antu a kasar Italiya, da kuma kasar Ghana a Afirka ta Yamma.

Shugaba Obama da iyalinsa sun komo gida jim kadan a bayan karfe 12 na daren asabar (watau asubahin lahadi).

A ranar asabar, shugaban na Amurka ya ka;lubalanci 'yan Afirka da su kara himmar kawar da talauci, yake-yake da kuma zarmiya da cin hanci a nahiyar.

A jawabin da yayi ga majalisar dokokin kasar Ghana, Mr. Obama yace ba a gudahnar da mulki na kwarai a wurare masu yawa a nahiyar Afirka. Ya ce kasashen Afirka ba su bukatar shugabanni masu neman dawwamar da kansu a karagar mulki, abinda suke bukata su ne cibiyoyi masu karfi da nagarta.

Wuri mafi sosa zuciya a wannan rangadi na shugaban a kasar Ghana shi ne tattakin da yayi zuwa wata tsohuwar cibiyar jigilar bayi, daga inda aka kwashi dubban 'yan Afirka a zamanin da aka tafi da su bauta a Amurka.

Kafin ya bar Ghana da maraicen asabar, Mr. Obama ya ce ba zai taba mantawa da yadda ya ga 'ya'yansa, jikokin 'yan Afirka da Amurkawa, suka wuce ta cikin kofar da a zamanin da duk wanda ya shige ta cikinta ya tafi ke nan, amma kuma suka komo.

Wannan ziyara a kasar Ghana ita ce ta farko da shugaban ya kai zuwa wata kasar bakar fatan Afirka tun lokacin da ya zamo shugaban Amurka na farko bakar fata.

A lokuta da dama a lokacin wannan ziyara ta sa a Ghana, shugaban ya ce ba wai Afirka dabam take da sauran duniya ba, bangare ce muhimmiya a duniyar yau da ta zamo kamar gari guda.

Ya ce ya zabi kai ziyara kasar Ghana a saboda yadda dimokuradiyyarta ke aiki, da kuma shugabanta, John Atta Mills, wanda Mr. Obama ya ce da gaske yana kokarin rage zarmiya da cin hanci.

XS
SM
MD
LG