Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hallaka Mutane 22 A Kazamin Fada Jumma'ar Nan A Babban Birnin Somaliya


'Yan tawaye masu kishin Islama a Mogadishu, babban birnin Somaliya, sun kaddamar da farmaki a kan sojojin gwamnati da na rundunar kiyaye zaman lafiya ta tarayyar Afirka, kafin ketowar alfijir jumma'ar nan, abinda ya haddasa mummunan fadan da ya kashe mutane akalla 22.

Mazauna birnin da suka firgita da irin kazamin fadan da ake gwabzawa, sun yi ta neman mafaka a yayin da ake musanyar wuta a kewayensu, kwanson bam na fadawa a kan gidajen jama'a, ana kuma musanyar wuta da manyan bindigogi.

Shaidu da jami'an birnin sun ce akasarin wadanda suka mutu fararen hula ne. An ce wasu mutanen su akalla 40 sun ji rauni.

Gwamnati da kungiyoyin sojan sa kai masu goyon bayanta, su na gwabza kazamin fada da kungiyoyi masu kishin Islama a karkashin jagorancin al-Shabab, domin sake kwato yankuna masu yawa na kasar da 'yan tawaye suka mamaye.

Shaidu a Beledweyne sun ce jumma'ar nan daruruwan sojojin kasar Ethiopia cikin damara da manyan makamai sun kutsa cikin wannan muhimmin gari dake bakin iyaka. Beledweyne yana cikin yankin Hiraan mai iyaka da kasar Ethiopia.

Wani dattijo mai suna Mohammed Ahmed Hoshow a garin ya ce sojojin na Ethiopia ba su fuskanci artabu ba a saboda sojojin sa kai masu adawa da gwamnati sun tsere daga garin. An kasa jin ta bakin jami'an gwamnatin Ethiopia dangane da wannan lamarin.

A ranar alhamis, wani kakakin gwamnatin Ethiopia, Bereket Simon, ya musanta ikirarin cewa sojojin Ethiopia su na da hannu dumu-dumu a yakin basasar Somaliya. Amma kuma ya tabbatar da labarin cewa an kyale sojojin sa kai na somaliya masu goyon bayan gwamnati su na amfani da yankunan kasar Ethiopia wajen kai farmaki a kan 'yan tawaye a cikin Somaliya.

XS
SM
MD
LG