Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Hamidu Karzai da Babban Abokin Hamayyarsa Duk Sun Fito Su Na Ikirarin Samun Nasara


Kwamitocin yakin neman zaben manyan 'yan takara biyu a zaben shugaban kasa na Afghanistan duk sun fito su na ikirarin samun nasara. Amma hukumar zabe ta kasar ta ce har yanzu babu tabbas a kan ko wanene ya lashe zaben na alhamis.

Jami'an yakin neman zaben shugaba Hamidu Karzai sun ce ratar da ya bayar tana da yawan da ba za a bukaci gudanar da zagaye na biyu na zaben fitar da gwani ba. Wani kakakin babban abokin hamayyar Karzai, tsohon ministan harkokin waje Abdullah Abdullah, shi kuma yayi ikirarin cewa dan takararsu ne ke da rinjaye.

Amma kuma, sakatare janar na hukumar zabe mai zaman kanta, Daoud Ali Najafi, yace ba a kidaya dukkan kuri'un da aka kada ba, saboda haka babu wanda zai iya ikirarin samun nasara. An kammala kidaya akasarin kuri'un, amma sai a yanzu ne ake kai su Kabul, babban birnin kasar inda za a tattara a lissafa.

Sai a farkon mako mai zuwa ne ake sa ran za a fara samun sakamakon zaben.

A muhimmin bayani na farko da aka samu daga 'yan kallo a zaben, Cibiyar Republican ta Amurka ta fada a yau jumma'a cewa an kamanta gaskiya a wannan zabe. Amma kuma jagoran 'yan kallon cibiyar da aka tura Afghanistan, Richard Williamson, yace akwai manyan matsalolin da aka fuskanta.

Yace rashin tsaro sosai ya rage yawan mutanen da suka fito, kuma an samu rahotanni masu tushe na sayarda katunan rajistar jefa kuri'a. Har ila yau Williamson yace an samu matsala da tawadar nan da ake amfani da ita don tabbatar da cewa mutum bai jefa kuri'a fiye da sau daya ba.

Duk da barazanar da 'yan Taliban suka yi ta kai hare-hare, 'yan Afghanistan da yawa sun fito suka kada kuri'u a zaben shugaban kasa na biyu a kasar. An kashe mutane akalla 26 a tashin hankali a Kabul da Kandahar da wasu manyan biranen kasar.

XS
SM
MD
LG