Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata Edward Kennedy Ya Rasu


Sanata Edward Kennedy, daya daga cikin 'yan majalisar dokokin da suka fi jimawa kan kujera kuma mafiya tasiri a duk tarihin Amurka, ya bar duniya yana da shekaru 77 da haihuwa. Marigayin, kani ne ga marigayi shugaba John F, Kennedy na Amurka.

Iyalan Kennedy suka ce ya bar duniya cikin daren talata a gidansa dake wani dan karamin gari mai suna Hyannis Port a bakin teku a Jihar Massachusetts. Sanata Kennedy, dan jam'iyyar Democrat, yayi shekara guda da watanni yana fama da wata irin cutar sankarar kwakwalwa da ba ta da magani.

Rashin lafiyar ya sa ba ya iya halartar zaman majalisar dattijai akasarin wannan shekara. Wannan ya sa daga gidan nasa yake ci gaba da kokarin ganin ya cimma gurinsa na babban batun da ya fi damunsa, watau kafa tsarin kula da lafiyar jama'a na kasa baki daya.

Edward Kennedy, ya wakilci Jihar Massachusetts a majalisar dattijai tun daga shekarar 1962, lokacin da aka zabe shi domin maye gurbin yayansa John Kennedy wanda ya zamo shugaban kasa. A lokacin da yake rike da wannan kujera kuwa, shi ne babban jigon bangaren masu ra'ayin sassauci, inda ya rungumi batutuwan da ya fi damunsu kamar hakkin 'yan tsuraru, ilmi da shige da ficen baki, da kuma tsarin kiwon lafiyar jama'a. A lokuta da dama, yana hada kai da 'yan jam'iyyar Republican domin tabbatar da cewa an zartas da wata doka.

A cikin wannan watan ne shugaba Barack Obama, wanda ya samu goyon bayan sanata Kennedy lokacin yakin neman zaben 2008, ya ba marigayin lambar yabo ta "Presidential Medal of Freedom". Kennedy bai samu halartar bukin ba shi wannan lambar yabon da aka yi a fadar White House ba.

XS
SM
MD
LG