Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Talata Za A Fara Sake Kidaya Dukkan Kuri'un Shugaban Kasa A Gabon


A yau talata kotun tsarin mulki ta kasar Gabon zata fara sake kidaya dukkan kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa na ranar 30 ga watan Agusta. ‘Yan takarar da suka sha kaye a zaben ne suka bukaci da a sake kidayar, a bayan da dan takarar jam’iyya mai mulki, Ali Ben Bongo, ya samu gagarumar nasara.

'Yan adawa sun yi zargin cewa magoya bayan Bongo sun tabka magudi, su na kuma fatar sake kidaya kuri’un zai kai ga soke wannan sakamako. Amma akasarin masu fashin bakin siyasa sun ce zai yi matukar wuya sake kidaya kuri’un ya sauya sakamakon. Suka ce akasari an nuna gaskiya a lokacin zaben duk da dan abinda ba za a rasa ba.

Tarzoma ta barke na wani dan karamin lokaci a Libreville, babban birnin kasar, da kuma birnin Port Gentil, a bayan da aka bayyana sakamakon wannan zabe. Gwamnati ta ce an kashe mutane uku a tarzomar. 'Yan adawa suka ce wadanda suka mutu sun kai akalla 15.

XS
SM
MD
LG