Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Guinea-Conakry Sun Kashe Mutane Akalla Hamsin Da Takwas Cikin Masu Zanga-Zanga


Shaidu da jami’an kiwon lafiya sun ce an kashe mutane akalla hamsin da takwas a kasar Guinea, a arangamar da aka yi a tsakanin dakarun tsaro da ‘yan adawa, wadanda suka yi ko oho da haramcin gwamnati suka gudanar da zanga-zanga. An yi wannan artabu jiya litinin a Conakry, babban birnin kasar.

Wakiliyar Muryar Amurka, Ricci Shryock, ta ambaci shaidu su na fadin cewa sojojin kurfau sun yi harbi kan masu zanga zangar da suka yi gangami a babban filin wasa na Conakry, domin nuna adawarsu da shirin shugaban gwamnatin mulkin soja, Kyaftin Moussa Dadis Camara, na tsayawa takara a zaben da za a gudanar a kasar.

Dakaru sun yi kokarin hana mutane shiga filin wasan a saboda gwamnatin mulkin soja ta haramta duk zanga-zanga kafin bukukuwan tuna ranar samun ‘yancin kai da za a yi ranar jumma’a. Amma wata gamayya ta kungiyoyin al’umma da jam’iyyun siyasa da kungiyoyin kwadago sun ce allambaram sai sun yi gangami.

Shi dai Camara ya kwace mulki a watan Disamba, ‘yan sa’o’i kadan a bayan mutuwar shugaba Lansana Conte. Jim kadan bayan da ya kwace mulkin, yayi alkawarin cewa zai gudanar da zabe na gaskiya kuma ba zai tsaya takara a zaben ba. Amma tun bayan wancan lokacin, majalisar mulkin soja ta ce kowa na iya tsayawa takara. Shi kansa Kyaftin Camara ya fada a watan da ya shige cewa ba zai kunyata magoya bayansa dake ta nemansa ya tsaya takara ba.

Daga can Abidjan kuma, wakilin Muryar Amurka Scott Stearns yace Kyaftin Camara yana kokarin ya nisanta kansa da harbe mutane akalla 58 da jami’an tsaro suka yi jiya litinin a Conakry.

Ya fadawa gidan rediyon RFM na Senegal cewa bai ji dadi ba, da aka ba shi labarin mace-mace a wajen gangamin masu yin adawa da tsayawarsa takara.

A bayan kashe-kashe da raunukan da mutane suka samu a hannun jami’an tsaron, an kuma kama shugabannin adawa aka dauke su zuwa babban barikin soja na Gini. Kyaftin Camara yace ya tambayi halin da shugabannin adawar suke ciki, kuma an tabbatar masa da cewar su na cikin koshin lafiya.

Zanga zangar nuna kin jinin shiga takara da Kyaftin Camara ke shirin yi ita ce mafi girma tun hawarsa kan mulki. Kuma ita ce mafi zub da jini. Ba za a iya tantance zahirin yawan mutanen da suka mutu ba a saboda an ce sojoji su na kwashe gawarwakin su na tafiya da su.

XS
SM
MD
LG