Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Kai Wasan Karshe Na Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya Na Matasa A Masar


‘Yan kwallon kafar matasa na kasar Ghana sun yi waje-rod da ‘yan wasan kasar Hungary da ci 3-2 domin kaiwa ga wasan karshe na cin kofin duniyar matasa ‘yan kasa da shekara 20 a Masar.

Abeiku Quansah shi ne ya jefa kwallo na uku da ya ba Ghana nasara a minti na 81 da fara wasa. Dominic Adiyiah, wanda shine ya fi kowa jefa kwallaye a wannan gasa baki daya, ya jefa kwallaye har guda biyu tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Wannan shine karo na uku da Ghana take kaiwa wasan karshe a wannan gasa ta ‘yan kasa da shekara 20. Ghana dai zata yi kokarin lashe wannan kofin a karon farko, domin a bayyanar da ta yi a wasannin karshe a 2001, ta sha kashi a hannun Ajantina, a 1993 kuma Brazil ce ta doke ta.

A wannan karo na ukun ma, Ghana zata kara ne da kasar Brazil, wadda ta cire kasar Costa Rica da ci daya mai ban haushi.


XS
SM
MD
LG