Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Talata Kungiyar ECOWAS Za Ta Bayyana Dakatar Da Jamhuriyar Nijar Daga Cikin Kungiyar


A yau talata Kungiyar Tarayyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, zata ba da sanarwar dakatar da Jamhuriyar Nijar daga cikin wannan kungiya. Haka kuma, ana sa ran Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka, da Kungiyar Tarayyar Turai, da kuma Majalisar Dinkin Duniya zasu bi sahun ECOWAS wajen kakabawa Nijar takunkumi.

Wakilin Muryar Amurka, Peter Clottey, ya ce wannan matakin, ya biyo bayan kiyawar da shugaba Mamadou Tandja yayi ya dakatar da zaben majalisar dokokin da gwamnatinsa ta shirya gudanarwa yau talata.

A karshen mako, wata tawagar kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin shugaba Ellen Johnson-Sirleaf ta kasar Liberiya, ta tattauna da shugaba Tandja a Niamey. Amma kuma gwamnatinsa ta ki yarda ta dakatar da zaben, tana mai cewa lokaci ya kure ma soke wannan zabe. ‘Yan hamayya a Nijar sun ce wannan ikirari zancen banza ne kawai.

A hiraras da VOA, darektan harkokin siyasa na kungiyar ECOWAS, Abdul Fatau Musah, yace kungiyar tana son daukar kwararan matakai a kan gwamnatin shugaba Tandja, yana mai cewa, "Tuni ECOWAS ta shirya fitar da sanarwa ta dakatar da Nijar. Taron koli na musamman na ba-zata da ECOWAS ta gudanar ranar 17 ga watan Oktoba ya yanke shawarar tura tawaga zuwa Nijar domin shawo kan hukumomi su dakatar da wannan zabe da muka yi imani da cewa na haramun ne, na gardama ne, kuma wanda ba zai kai ga sasanta al’ummar kasar ba."

Darektan harkokin siyasar na ECOWAS ya ce shugaba Tandja, ya kekasa kasa ya ki yarda da yunkurin kungiyar na neman ya dakatar da wannan zabe. Ya ce, "Shugaba Tandja, a ta sa irin hikimar, ya ki karbar shawarar da aka ba shi ta dakatar da wannan zaben, kuma a yanzun nan da muke magana, ana can ana kokarin yin wannan zabe." Abdul Fatau Musah, yace ita kuma kungiyar ECOWAS zata dauki matakin da ta ce zata dauka. Ya ce da ma dai, taron kolin ECOWAS ya yanke shawarar cewa idan Tandja ya ki yarda da shawarwarin da wannan taro ya bayar, to nan take za a kafa ma kasar Njijar takunkumi.

Abdul Fatau Musah na ECOWAS yace kungiyar ta damu da rikicin siyasar dake dabaibaye Jamhuriyar Nijar. Ya bayyana cewa, "Duk wata harkar siyasar da ake gudanarwa yanzu haka a Jamhuriyar Nijar ta saba ma doka, haramun ce a bisa tsarin mulkin kasar. Babu wanda yake tababar hakan. A saboda haka muka dakatar da Nijar daga duk wata harka ta ECOWAS. A yanzu Nijar ba memba ce ta ECOWAS ba, kuma ba zata kasance memba ba har sai bayan an kawar da wannan abu na haramun da aka yi a kasar, aka maido da yin aiki da tsarin mulki na 1999. Wannan shine abu mafi kankanci da ECOWAS take nema daga wurin shugaba Tandja.

darektan siyasar na ECOWAS ya ce kungiyarsu tana kuma neman Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka da ta sanya takunkumi mai tsauri a kan Nijar, inda ya ce "Tuni har ECOWAS ta fara kokarin mika takardun bayaninta kan Jamhuriyar Nijar ga Kungiyar tarayyar Kasashen Afirka da kuma Majalisar Dinkin Duniya domin su ma su dauki matakin da ya dace kai....Ta hanyar mu’amalar da muke yi da kawayenmu kuma, na fahimci cewa Kungiyar Tarayyar Turai ta saka jamhuriyar Nijar karkashin sashe na 96 na Yarjejeniyar Cotonou, sashen da tuni ya ayyana takunkumi na dukkan kasashen Tarayyar Turai a kan Nijar din har sai ta wanzar da wani mizani na dimokuradiyya.

Hukumomin Nijar dai su na ta shirye-shiryen gudanar da wannan zabe na yau talata, duk da cewa ‘yan hamayya su na kaurace ma zaben, kuma kasashen duniya su na yin Allah wadarai da shi.


XS
SM
MD
LG