Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samarin Najeriya Sun Kai Ga Wasan Karshe


Mai masaukin baki Najeriya da kuma Switzerland sun samu kaiwa ga wasan karshe na cin kofin kwallon kafar duniya na samari 'yan kasa da shekara 17 wanda ake bugawa yanzu haka a Najeriya.

Najeriya ta yi kaca-kaca da samarin kasar Spain da ci Uku da daya. Dan wasan Najeriya mai suna Sani Emmanuel, wanda ya shigo wasa daga baya, ya jefa kwallaye har guda biyu a raga, ta farko a minti na 61 da fara wasa, na biyun kuma a cikin minti na 71 da fara wasa. Stanley Okoro shi ya fara jefa ma Najeriya kwallo a raga a minti na 30 da fara wasa. Spain ta jefa kwallonta kwaya daya tak a raga a minti na 81 da fara wasa.

Najeriya ce ta ke rike da wannan kofi da ta ciwo a gasar baya da aka yi a 2007, inda a can ma ta doke Spain a wasan karshe. A wannan karon, 'yan wasan Najeriya, wadanda ake kira "Golden Eaglets", za su yi karon-batta ne da 'yan wasan kasar Switzerland wadanda suka gwabje takwarorinsu na kasar Colombia da ci hudu da babu a wasansu na kusa da karshe.

Wannan shi ne karon farko da 'yan wasan kasar Switzerland suke zuwa wannan gasa, kuma ga shi a karonsu na farko sun kai ga wasan karshe. A bayan haka ma, wannan shi ne karon farko da kasar Switzerland zata buga wani wasann karshe wanda Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta shirya tun lokacin da kasar Uruguay ta doke ta da ci 3 da babu a Gasar Kwallon kafa ta Olympics a shekarar 1924, watau shekaru tamanin da biyar (85) da suka shige ke nan.

XS
SM
MD
LG