Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Alhamis Za A Rantsar Da Shugaba Hamid Karzai Na Afghanistan


A yau alhamis za a rantsar da shugaba Hamidu Karzai na Afghanistan domin fara wa’adinsa na biyu kan mulki, yayin da kasashen yammaci ke matsa masa lambar ya yaki zarmiya da cin hanci, ya kuma kyautata yadda ake gudanar da mulki.

An dauki tsauraran matakan tsaro a Kabul, babban birnin kasar, domin bukin rantsarwar da za a gudanar a gaban baki na kasashen waje da shugabannin Afghanistan a harabar fadar shugaban kasa dake da tsaro sosai.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta isa Kabul jiya laraba, tana mai fadin cewa sabon wa’adin shekaru biyar da shugaba Karzai zai fara a kan karagar mulki, wata sabuwar dama ce ga shugabannin Afghanistan su kulla sabon alkawari da jama’arsu.

A jiya larabar kuma, shugaba Barack Obama na Amurka ya ce nan da wasu ‘yan makonni zai bayyana sabuwar dabarar yaki da kuma aniyar Amurka a Afghanistan.

Shugaba Obama ya ce sabuwar manufar zata yi magana a kan dukkan fannonin dabarun yaki na Amurka a Afghanistan, inda ya ce, “Ina da kwarin guiwar cewa a karshen zaman sake nazari da shawarwarin, zan iya gabatarwa da Amurkawa irin abubuwan da muke fuskanta a zahiri, da abubuwan da muke da aniyar yi, da matakan da muke son dauka da muke ganin zasu kai mu ga nasara, da yawan kudin da zamu kashe, da kuma tsawon lokacin da muke jin zamu yi."

Shugaba Obama yace yana son idan sojojin Amurka sun kammala aikinsu a can, ya zamanto sun bar kasar Afghanistan cikin kwanciyar hankali.

XS
SM
MD
LG