Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliyawa 'Yan Fashi A Teku Sun Sake Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Amurka Da Suka Taba Kamawa


‘Yan fashi cikin teku na Somaliya sun kai farmaki a karo na biyu cikin watanni bakwai a kan wani jirgin ruwan Amurka, amma a wannan karo, masu gadi na jirgin sun fatattake su.

Jiya laraba da sanyin safiya ‘yan fashin suka kai farmaki kan wannan jirgin ruwa mai suna "Maersk Alabama", jirgin da suka taba yin fashinsa a cikin watan Afrilu inda suka kama kyaftin na jirgin, Richard Phillips, suka yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki biyar.

Rundunar ta Biyar ta mayakan ruwan Amurka, mai hedkwata a kasar Bahrain, ta ce ‘yan fashi su hudu a cikin irin kananan kwale-kwalen nan masu gudu, sun zo har dab da wannan jirgin ruwan daukar kwantena mai tafe da tutar Amurka, a yayin da yake tafiya a wani wuri mai tazarar daruruwan kilomitoci a arewa maso gabas da gabar Somaliya.

Rundunar mayakan ruwan ta ce ma’aikatan jirgin sun dauki matakan kariya ciki har da yin amfani da wata na’ura mai tsananin kara domin birkita lissafin ‘yan fashin, karar da kunnuwan dan Adam ba su iya jure ta. Har ila yau sun yi amfani da bindigogi kanana a lokacin da ‘yan fashin suka bude wuta.

Ba a samu rahoton mutuwa ba, haka kuma ‘yan fashin ba su samu sukunin shiga jirgin ruwan na Amurka ba.

XS
SM
MD
LG