Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Miliyoyin Musulmi Mahajjata Suke Hawan Arafat, Yayin Da Ruwan Sama Ya Kashe Mutane 11


Ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma ambaliyar da ya haddasa, sun kashe mutane akalla 11 jiya laraba a Sa’udiyya, a yayin da miliyoyin Musulmi suka shiga haramar fara aikin Hajjin bana.

Ruwan da aka shafe tsawon rana jiya laraba ana tabkawa, ya kawo ambaliya a kan tituna, ya haddasa cunkoson ababen hawa, ya katse wutar lantarki, ya kuma sa mutane suka kasa fita daga cikin gidajensu. Wasu mahajjatan sun kasa samun hanyar wucewa a yayin da suka doshi birni mai Tsarki na Makka daga birnin Jeddah.

Mutanen da suka samu isa wurare masu tsarki ba su kai na shekarun baya ba ya zuwa jiya larabar.

A jiyan, mahajjata cikin harami sun yi dawafi a dakin Ka’abah mai tsarki. Ana sa ran mahajjata miliyan biyu da rabi ne zasu yi aikin Hajjin bana, yayin da hukumomi suke aiki ka’in da na’in don kawar da damuwa game da cutar murar aladu da kuma tsaron lafiyar mahajjatan.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya bada sanarwa jiya laraba, yana mika sako na fatar alheri ga Musulmin dake aikin Hajji a Sa’udiyya tare da taya illahirin Musulmi na duniya murnar Sallar layya da za a yi kwana guda bayan hawan Arafat.

Shi ma babban kwamandan sojojin Amurka da na NATO a Afghanistan, Janar Stanley McChrystal, ya aike da sakon Barka da Sllah ga Musulmi ya kuma yi kira ga al’ummar Afghanistan da su yi aiki da akidojin addinin Musulunci kamar gaskiya, da halin kwarai da adalci da kuma ‘yanci don sake gina kasar Afghanistan.

XS
SM
MD
LG