Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Fiye Da Wata Shida Ba A Biya Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Dake Somaliya Albashinsu Ba


Wakilin Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka, KTKA, a Somaliya yace rabon da a biya sojojin kiyaye zaman lafiya dake kasar albashinsu tun watan Mayu, watau fiye da watanni shida da suka shige.

Nicolas Bwakira ya fada jiya laraba cewa kasashe masu bayar da agaji sun bayar da wani gutsuri ne kawai na kudaden da suka yi alkawarin bayarwa wata da watannin da suka shige don karfafa tsaro a Somaliya. A watan Afrilu, masu bayar da agaji sun yi alkawarin bayar da kudi fiye da dala miliyan 250 domin kara yawan sojojin KTKA da na gwamnatin Somaliya a cikin kasar.

Bwakira yace rashin bayar da kudin yana gurgunta aikin Tarayyar Afirka a Somaliya, yayin da guiwoyin sojojin kiyaye zaman lafiyar da na gwamnatin Somaliya duk sun yi sanyi.

Akwai sojojin KTKA su kimanin dubu 4 daga Uganda da Burundi su na taimakawa wajen kare gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya daga hare-haren 'yan tawayen dake son kafa jamhuriyar Islama. Sojojin kiyaye zaman lafiyar akasari su na gadin muhimman wurare ne kamar filin jirgin saman Mogadishu, da tashar jiragen ruwa da kuma fadar shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG