Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa Na Nijeriya Yana Fama Da Ciwon Kumburin Zuciya


Wani kakakin shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa na Nijeriya ya ce shugaban yana jinyar wata irin cuta ta zuciya.

Olusegun Adeniyi ya fadawa 'yan jarida alhamis a Abuja cewa shugaba 'Yar'aduwa yana fama da wata irin cuta mai tsanani ta kumburar zuciya wadda ake kira "Pericarditis" a turance.

Ya ce shugaban yana murmurewa sosai daga jinyar wannan cuta da ake yi masa a wani asibiti a birnin Jeddah dake kasar Sa'udiyya.

A ranar litinin aka kai shugaban na Nijeriya Jeddah domin gwaje-gwaje da kuma jinya. Kakakin ya ce a ranar Jumma'a da ta shige 'Yar'aduwa ya fara kokawa cewar yana jin wani irin ciwo mai zafi a kirjinsa.

Wannan shi ne karo na uku cikin watanni uku da ake kai shugaban na Nijeriya zuwa Sa'udiyya.

An san cewa shugaba 'Yar'aduwa, mai shekaru 58 da haihuwa, yana fama da wata cuta mai tsanani ta koda. Lalacewar koda da daina aikinta a jikin mutum, na iya haddasa irin wannan cuta ta kumburin zuciya da shugaban na Nijeriya ke jinyarta a yanzu.

'Yar'aduwa ya zamo shugaban Nijeriya a bayan zaben 2007 da aka yi gardama kan sakamakonsa. Masu sukar lamiri sun bayyana cewa ba ya da koshin lafiyar da zai iya jagorancin kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka.

XS
SM
MD
LG