Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Nada Ibrahim Gambari A Zaman Shugaban Ayyukan Kiyaye Zaman Lafiya A Darfur


Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta bayar da sanarwar cewa jami'in diflomasiyya na Nijeriya, Ibrahim Gambari, zai zamo sabon shugaba mai kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya na hadin guiwa na majalisar da kuma Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka, KTKA, a yankin Darfur na kasar Sudan.

Babban sakataren MDD, Ban Ki-moon, ya ce Gambari zai karbi ragamar sabon mukamin nasa a ranar 1 ga watan Janairu.

A yanzu dai Gambari shi ne wakilin MDD na musamman a kasar Burma, kuma mashawarci a kan Iraqi. Wata mai magana da yawun majalisar ba ta ambaci ko wanene zai maye gurbin Gambari a mukaman da zai ajiye ba.

A can baya, Gambari ya taba rike mukaman na'ibin sakatare janar na MDD mai kula da harkokin siyasa, da mai ba da shawara ga majalisar kan harkokin Afirka, ya kuma taba zama jakadan Nijeriya a Majalisar.

XS
SM
MD
LG