Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Addini Na Iran Ya Zargi 'Yan Hamayya Da Neman Gurgunta Tsarin Islama A Kasar


Shugaban addini na kasar Iran ya zargi 'yan hamayya masu ra'ayin sauyi da laifin gurgunta tsarin Islama a kasar tare da cin zarafin mutumin da ya kafa jamhuriyar Islama ta Iran.

Lahadin nan, Ayatollah Ali Khameini yace zanga-zangar da 'yan hamayya suke ci gaba da yi nuna rashin mutunci ne.

Gidan telebijin na kasar ya nuna hotunan bidiyo na wadanda yace magoya bayan 'yan hamayya ne su na lalata hotunan Ayatollah Khameini, da kuma mutumin da ya kafa jamhuriyar Islama, Ayatollah Ruhollah Khomeini, lokacin wata babbar zanga-zangar da suka yi ranar 7 ga watan Disamba.

A yau lahadi rundunar zaratan sojojin Iran ta "Revolutionary Guard" ta yi kiran da a hukumta 'yan zanga zangar da suka yaga ko suka kona hotunan marigayi Ayatollah Khomeini.

Jiya asabar, malamai na kasar Iran masu ra'ayin karfafa tsarin addini sun yi zanga-zanga a biranen kasar domin yin tur da dalibai masu ra'ayin sauyi da suka gudanar da munanan zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati. A birni mai tsarki na Qom, Ayatollah Ahmad Khatami, ya zargi 'yan hamayya da kokarin rusa tsarin gwamnatin Islama ta kasar Iran.

XS
SM
MD
LG