Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru A Philippines Sun Ce Narkakken Dutse Na Ci Gaba Da Taruwa A Tumbin Dutse Mai Aman Wuta Na Mayon


Kwararru a kasar Philippines sun ce narkakken dutse na ci gaba da taruwa a tumbin dutsen Mayon mai aman wuta, abinda ka iya haddasa fashewar dutsen cikin 'yan kwanaki.

A yau asabar, shugaban gungun masana da gwamnatin Philippines ta tura domin sanya idanu a kan dutsen, Ed Laguerta, yayi gargadin cewa koda yake yawan girgizar kasar dake faruwa a can karkashin dutsen ya ragu, tana iya yiwuwa a samu babbar girgizar da zata sa dutsen ya fara amai yana cilla narkakken dutse da toka da hayaki sama.

Mutane kusan dubu hamsin da aka kwashe daga gindin dutsen sun shafe hutun Kirsimeti a cibiyoyin tsugunarwa da aka kafa a yayin da dutsen na Mayon yake barazana ga gidajensu. Gwamnatin lardin ta rarraba abinci da kyaututtuka ga mutanen da suke zaune a wadannan cibiyoyi.

A ranar alhamis da daddare an gudanar da tarurrukan ibada a cibiyoyin yayin da toka mai kamar dusar kankara take ci gaba da rufe yankin dake kewayen dutsen.

XS
SM
MD
LG