Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 30 A Kazamin Fada Tsakanin Kungiyoyin Tawaye Biyu A Yankin Tskiyar Somaliya


Adadin mutanen da aka kashe a wani kazamin fadan da ake gwabzawa tsakanin wasu kungiyoyi 'yan tawaye biyu na ‘yan kishin Islama a yankin tsakiyar kasar Somaliya ya karu zuwa akalla 30.

Kungiyar ‘yan tawayen al-Shabab ta kai farmaki kan garin Dhusamareb jiya asabar, tana kokarin kwace shi daga hannun kungiyar Ahlu Sunna wal Jama’a mai goyon bayan gwamnatin Somaliya.

Jiya asabar da dare, kungiyar al-Shabab ta yi ikirarin kama garin, amma Ahlu Sunna ta ce ta fatattaki ‘yan al-Shabab ta kuma kashe mayakan kungiyar da dama.

Rahotannin dake fitowa daga garin yau lahadi sun ce an kashe mutane akalla 30, wasu da dama suka ji rauni a wannan fada.

Wannan shi ne fadan farko da aka gani a garin na Dhusamareb tun cikin watan Disambar 2008 a lokacin da Ahlu Sunna ta kwace shi daga hannun ‘yan al-Shabab.

XS
SM
MD
LG