Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uganda Ta Ce Sojojinta Sun Kashe Wani Babban Kwamandan 'Yan Tawaye


Rundunar sojojin Uganda ta ce dakarunta sun kashe wani babban kwamandan kungiyar 'yan tawaye ta "Lords Resistance Army" ko LRA a takaice.

Hafsoshi sun ce ranar jumma'a aka kashe janar Bok Abudema lokacin wani farmaki a yankin kudu maso gabashin kasar Afirka ta Tsakiya a kusa da garin Djema. An yi imanin cewa Abudema shi ne mukaddashin kwamandan kungiyar, kuma shi ne tamkar wazirin madugun kungiyar ta LRA, Joseph Kony.

Wani kakakin rundunar sojojin Uganda, leftana kanar Felix Kulayigye, ya bayyana kashe Abudema da aka yi a zaman wani "goron sabuwar shekara ga al'ummar Uganda."

Sojojin Uganda su na farautar mayakan kungiyar LRA a duk fadin yankin tsakiyar Afirka tare da iznin gwamnatocin kasashen yankin. Ana zargin cewa Kungiyar 'yan tawayen, wadda a da take da cibiya a arewacin Uganda, ta kashe, ta sace ko kuma ta yanke gabobin dubban mutane a cikin shekaru 20 da suka shige.

XS
SM
MD
LG