Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Dan Jaridar Britaniya  A Afghanistan


Jami'an Britaniya sun ce wani bam da ya tashi a gefen hanya a kudancin Afghanistan ya kashe wani dan jarida na Britaniya da sojan Amurka daya da kuma wani sojan dan Afghanistan.

Ma'aikatar tsaron Britaniya ta ce wakilin harkokin tsaro na Jaridar Sunday Mirror, Rupert Hamer, ya mutu, mai daukar hoto nasa, Philip Coburn, ya ji mummunan rauni a lokacin da motar da suke tafiya ciki tare da sojojin kundumbala na Amurka ta taka wani bam da aka dasa a gefen hanya jiya asabar.

An bayar da rahoton cewa wasu sojojin kundumbalar su 4 sun ji munanan raunuka.

A halin da ake ciki, hukumomin Amurka da na Afghanistan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar mika wa Afghanistan nauyin gudanar da gidan kurkukun dake sansanin mayakan sama na Bagram nan da karshen wannan shekara. Ma'aikatar tsaron Afghanistan ta sanar jiya asabar cewa nan bada jimawa ba za a fara horas da sojojin Afghanistan ta yadda zasu karbi ragamar bincike da tsarewa da kuma shari'ar fursunonin dake gidan kurkukun.

XS
SM
MD
LG