Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Umaru Musa 'Yar'aduwa Yace Shugaban Yana Nan Da Rai


Wani kakakin shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa na Nijeriya ya musanta rade-radin cewa shugaban ya mutu ko kuma dai yana cikin suma a bayan da ya shafe makonni yana jinya a asibiti a kasar waje.

Olusegun Adeniyi ya fada wa 'yan jarida litinin cewa 'Yar'aduwa, "yana nan da ransa, kuma yana ma samun sauki." Ya ce shugaban "yana cikin hayacinsa, yana magana, har ma yayi magana" da jami'an gwamnatin Nijeriya ta wayar tarho.

Rabon da jama'a su ga shugaba 'Yar'aduwa da idanunsu, ko kuma su ji maganarsa, tun karshen watan Nuwamba, lokacin da aka kai shi wani asibiti a birnin Jeddah, a kasar Sa'udiyya.

Furucin kakakin yana zuwa kwana guda kafin wata kotun tarayya a Nijeriya da kuma majalisar dokokin kasar su tattauna rashin kasancewar shugaban a cikin Nijeriya.

Kotun zata saurari wasu kararraki guda uku dake neman tilasta mika mulkin kasar ga mataimakin shugaba Goodluck Jonathan.

Haka kuma talata ne maasu zanga-zangar neman kawo karshen wannan rudu game da halin da shugaba 'Yar'aduwa ke ciki za su gudanar da wani gangami a Abuja, babban birnin kasar.

An shirya gwamnonin Nijeriya zaus yi taron gaggawa cikin daren litinin a Abuja kan halin da shugaban yake ciki.

XS
SM
MD
LG