Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Mutuwar Mata Masu Juna A Nijeriya


Matsalar mace-macen mata da yara a lokacin ciki ko haihuwa dai ta jima ta na ci wa kasashe masu tasowa tuwo a kwarya.

Alal misali, a sa’ilin da a kasashen da suka ci gaba mata 7 zuwa 15 ne ke mutuwa a cikin mata masu juna 100,000 daga lalurar ciki ko haihuwa; amma a kasashe masu tasowa har wajen mata 100-300 ne kan rasu sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa.

Idan mun mayar da hankalinmu kan kasashe masu tasowa kuwa; kasar Indiya, wace ta fi yawan jama’a, ita ce din kuma ta fi yawan mace-mace na lalurorin ciki ko haihuwa, inda cikin mata masu juna biyu 100,000 mata wajen 117,000 ne ke halaka sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwar.

Na biya a mace-macen mata a kasashe masu tasowa da ma Duniyar baki daya ita ce Nijeriya, inda a cikin mata masu juna biyu 100,0000, wajen 59,000 ne ke rasuwa sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa.

Ma’ana, kullayaumin mata 137 na mutuwa sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa ko kuma a kowane awa daya mata 6 na mutuwa saboda lalurorin ciki ko haihuwa a Nijeriya.

Idan kuma mun mai da hankali kan Nijeriya, sai kuma mu ga cewa al’amarin ya fi karfi a Arewacin kasar, kuma a Arewar ma an fi samun matsalar ta mace-macen mata masu ciki ko haihuwa a Arewa maso gabas.

Matsalar ta mata masu ciki dai na matukar shafar jariransu. Kuma abin ya fi tsanani ne a wuraren da mace-macenna mata ya fi yawa.

Alal misali, a sa’ilinda jarirai 166 ne kadai cikin 100,000 da aka Haifa ke mutuwa a Kudu-maso-yammacin kasar; a Arewa maso gabashin kasar kuwa har wajen 1549 ne ke mutuwa.

To ko mene ne musabbabin yawan mutuwar mata din? Akwai dai dalilai da yawa. Kama daga zuwa asibiti cikin kurarren lokaci, zuwa rashin kyawun hayar zuwa asibitin, zuwa rashin magunguna masu kyau, zuwa rashin kudin zuwa asibitin da kuma wasu al’adun gargajiya masu nasaba da jahilci da dai sauransu.

Idan ba a manta ba dai kwanan nan Ministan Kiwon Lafiya na Nijeriya ya ziyarci wani magidancin a wani kauye a karamar Hukumar Lere ta Jahar Kaduna da ya karya kashin bayansa lokacin ya ke kokarin dawowa don ganin matarsa mai ciki da ta fadi daga mashin a daidai wata yar gada sanadiyyar rashin kyawun hanyar zuwa asibiti. Shi ma ya na kusa da gadar sai ya fadi ya karya kashin bayansa ta yadda a yanzu bai iya tashi. I ta ko matar tasa, da ta riga shi hadari ta mutu da jaririn a cikinta asibitin. Akwai dai ire-iren wannan abin takaicin a Nijeriya. To saidai hukumomin da abin ya shafa na ikirarin sun zaburo

XS
SM
MD
LG