Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Laka Da Kasa  Sun Goce Daga Tuddai Suka Rufe Kauyuka Da Daruruwan Mutane A Uganda


Wani jami'in Uganda ya ce kasa da lakar da suka goce daga wasu tuddai a yankin gabashin kasar sun kashe mutane akalla 106.

Karamin minista mai kula da ayyukan da suka shafi abkuwar bala'i, Mussa Ecweru, ya fadawa Sashen harshen Swahili na Muryar Amurka cewa har yanzu akwai mutane 300 wadanda ba a san abinda ya same su ba.

A bayan da aka shafe fiye da mako guda ana juye ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin Bududa dake kusa da dutsen Elgon, laka da kasa sun goce cikin daren litinin suka rufe kauyuka guda uku a yankin.

'Yan sanda da sojoji sun shiga cikin ayyukan nemo wadanda suka kubuta da rayukansu.

Jami'ai suka ce gocewar laka da kasar ta lalata gidaje da kasuwanni da makarantu da kuma wani asibiti.

XS
SM
MD
LG