Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Hamayya Da Gwamnatin Togo Kowanne Yana Ikirarin Shine Ya Sami Nasarar Zaben Shugaban Kasa


Ranar jumma’a a Togo, Jam’iyyar ‘yan hamayya da wacce take mulkin kasar dukkansu biyu suna ikarin samun nasara a zaben shugaban kasa da aka yi ranar Alhamis.

Madugun ‘yan hamayya Jean-Pierre Fabre, ya fada cewa sakamkon farko da Jam’iyyarsa UFC,ta tattara ya nuna yana kan gaba ,bayan an kidaya kamar kashi 75-80 na kuri’u da aka kadaa wasu sassan kasar.

Amma kakakin gwamnatin kasar pascal Bodjona,ya karyata wan ikirarin.Ya gayawa tashar radiyon Faransa cewa jam’iyya mai mulki RTPP,da shugaba Faure Gnassigbe ta sami abinda ya kira gagarumar nasara.Babban skaataren jam’iyyar RTPP Solitoki Esso,ya zargi fabre da kokarin hura wutan fitina cikin kasar.

Anasa ran yau zuwa gobe lahadi ce jami’an zabe zasu bada sakamkon zabe.

XS
SM
MD
LG