Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ce Har Yanzu Tana Jin Za A Yi Shawarwari Tsakanin Isra'ila Da Falasdinawa


Amurka ta ce ta yi imanin za a gudanar da shawarwarin neman zaman lafiya ,wanda ba na kai tsaye ba ne, a tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, duk da fusatar da larabawa suka yi kan shirin bani Isra’ila na fadada unguwannin yahudawa ‘yan share ka zauna a gabashin Qudus.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, P.J. Crowley ya fadawa ‘yan jarida jiya alhamis cewa Amurka ba ta samu wani bayanin cewa Falasdinawa sun yanke shawarar janyewa daga wannan tattaunawar shiga tsakani ba.

Crowley yace har yanzu wakilin Amurka a gabas ta tsakiya, George Mitchell, yana shirin tafiya yankin a mako mai zuwa domin shirya yadda za a yi tattaunawar wadda ba ta gaba da gaba ba ce.

Jami’an Falasdinawa sun ce ba zasu fara tattaunawa ba har sai Isra’ila ta dakatar da aikin gina gidaje ma yahudawa a yankunan Falasdinawan da ta mamaye..

A ranar talata Isra’ila ta bada sanarwar gina sabbin gidaje 1,600 a daidai lokacin da mataimakin shugaban Amurka Joe Biden yake ganawa da jami’an Isra’ila don bayyana goyon bayan Amurka ga farfado da shawarwarin neman zaman lafiya. Jiya alhamis, mataimakin shugaban na Amurka ya sake yin Allah wadarai da shirin na Isra’ila, amma yace ya kamata a fara shawarwarin neman zaman lafiya a tsakanin sassan ba tare da jinkiri ba.

XS
SM
MD
LG