Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsagera Sun Tayar Da Bam A Warri


Wasu bama-bamai guda biyu da aka dana cikin motoci sun tashi jiya litinin a birnin Warri a kudancin Nijeriya, a daidai lokacin da jami'ai suka taru don tattauna shirin ahuwa ga tsageran yankin.

Rahotanni daga wurin sun ce mutane akalla biyu sun ji rauni a lokacin da bama-baman biyu suka tashi, na biyun bayan minti talatin da tashin na farko, a dab da gidan gwamnatin Jihar Delta inda ake tattaunawa game da ahuwa ga tsageran yankin Niger Delta.

'Yan mintoci kadan kafin tashin bam na farko, babbar kungiyar tsagera a yankin Niger Delta ta aike da sakon Imel ga 'yan jarida tana gargadin cewa zata tayar da bam din.

Kungiyar tsagera ta MEND ta ce ta kai wannan harin ne domin tunaar da duniya cewa har yanzu tana nan daram dinta a yankin. Ta ce gwamnan Jihar Delta yayi watsi da wannan kungiya yana mai fadin cewa 'yan jarida ne kawai suka kirkire ta a rubuce-rubucensu.

XS
SM
MD
LG