Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliya Ta Yi Kisa Da Ta'adi A Angola Da Zambiya


Mutane akalla 12 suka mutu a Luanda, babban birnin Angola, a bayan da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya rushe gidaje da yawa.

Mukaddashin gwamnan Luanda, Bento Soyto, ya fada jiya litinin cewa cewa wasu mutanen da dama sun gudu daga gidajensu ala tilas a bayan da ambaliya ta mamaye wasu unguwanni.

Kamfanin dillancin labaran Reuters yace ruwan saman da ya zubo kamar da bakin kwarya ya kashe wasu mutanen su 8, ya sa daruruwan mutanen suka rasa gidajensu a Zambiya, makwabciyar Angola. Ambaliyar ruwa ta wanke hanyoyi da gadoji da kuma gine-gine a kasar ta Zambiya.

XS
SM
MD
LG