Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Ta Janye Jakadanta Daga Libya


Nijeriya Ta Janye Jakadanta Daga Libya
Nijeriya Ta Janye Jakadanta Daga Libya

<!-- IMAGE -->

Nijeriya ta janye jakadanta daga kasar Libya, a bayan da shugaba Mu'ammar Gaddafi ya ba da shawarar a kasa Nijeriya gida biyu, daya kasar Musulmi, daya kuma kasar Kirista domin a kawo karshen zub da jinin bambancin addini.

Jiya alhamis wani kakakin ma'aikatar harkokin Nijeriya ya bayyana kalamun shugaba Gaddafi a zaman marasa karbuwa. Yace irin wadannan kalamun ba su yi kama da na mutumin dake bayyana rajin hade kan nahiyar Afirka ba.

Shugaba Gaddafi ya fadawa taron dalibai na kasashen Afirka ranar talatar makon nan a birnin Tripoli cewa raba Nijeriya gida biyu zata ceci rayukan Musulmi da Kirista, zata kuma hana lalata Masallatai da majami'u.

Shi ma shugaban majalisar dattijan Nijeriya, David Mark, ya fito ranar laraba yana bayyana shugaban an Libya a zaman mahaukaci a saboda babatunsa na cewa a raba Nijeriya.

Nijeriya ta sha samun tashin hankali a tsakanin mabiya addinan biyu.

XS
SM
MD
LG