Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

    Kusan mutane miliyan biyu galibi yara yan kasa da shekaru biyar ne kan mutu duk shekara sanadiyyar gudawa.


    Kusan mutane miliyan biyu galibi yara yan kasa da shekaru biyar ne kan mutu duk shekara sanadiyyar gudawa.

<!-- IMAGE -->

Karanacin ruwa da kuma gurbacewarsa na dada tsananta a daidai lokacin da yawan jama'a ke karuwa masu bukatar a kara samar da ruwa sosai da sosai don sha da tsabtacewa da aikin gona da kuma masana'antu. Wannan al'amari ya janyo gagarimin kalubale ga al'ummomi dabam-dabam da yawansu ke ta karuwa da kuma dangantakarsu da muhallinsu.

Fiya da mutane miliyan dubu biyu da takwas ne za su kasance a sassan duniya da ke da karancin ruwa ko kuma ake ribibinsa ya zuwa shekara ta 2025. Adadin ruwan da ake bukata na ribanyuwa duk bayan shekaru 20.

Wuraren da halittu kan yi ma'amala da tsatataccen ruwa da kuma batun tattalin,muhallida suka dogara ga magudanan ruwa na ta kara fuskantar barazana daga harkokin dan adam na yau da kullum da su ka hada da janye ruwa da karkatar da madatsun ruwa da kuma aikace-aikacen raya birane da ma'aikatu da kuma gurbacewar muhalli.

Wurare masu danshi da halittu kan rayu da kuma kan zama garkuwa daga hadarurruka nay au da kullum da kuma wurin kiwon kifaye na ta bacewa a fadin duniyan nan cikin matukar sauri.

A kasashe masu tasowa kashi tasa'in da biyar cikin dari na ruwa mai datti na kwaranya zuwa inda jama'a ke zama ba tare da an diga ruwa maganin kashe cututtuka wa ruwan ba.

Fiye da mutane miliyan dubu ba su da sukunin ingantattun magudanan ruwa kuma fiye da mutane miliyan dubu biyu basu da sukunin ingantaccen tsarin tsabtace muhalli, wanda hakan ke yin nakasu ga sha'anin kare lafiyar jama'a.

Fiye da kashi 50 cikin dari na gadajen asibitocin da ke fadin duniyan nan wadan da suka kamu da cututtukan da ked a alaka da ruwa mara tsabta ne ke jinya a kai.

Kusan mutane miliyan biyu galibi yara yan kasa da shekaru biyar ne kan mutu duk shekara sanadiyyar gudawa.

Kashi saba'in cikin dari na ruwan da dan adam kan yi amfani da shi ana amfani da shi ne a aikin noma da sauran kayan abinci da akan yi nomansu, kuma wannan adadin ya ma fi yawa a kasashe masu tasowa.

· Kashi tasa'in cikin dari na mutuwar da annoba kan haddasa na da nasaba da ruwa.

XS
SM
MD
LG