Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sudan Ya Ja Kunnen Kudancin Kasar


Shugaban Sudan Ya Ja Kunnen Kudancin Kasar

<!-- IMAGE -->

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan yayi gargadin cewa idan har tsoffin 'yan tawayen Kudancin kasar suka kaurace ma zabubbuka na kasa da za a yi cikin wata mai zuwa, to yankin arewacin kasar ba zai yarda a gudanar da zaben raba-gardama a kan ballewar kudancin kasar ba.

Shugaba al-Bashir ya fadawa wani taro a birnin Khartoum cewa idan har jam'iyyar SPLM mai mulkin Kudancin Sudan ta ki shiga cikin zabubbukan na kasa, to ba za su yarda a gudanar da kuri'ar raba-gardamar ba.

Amma tun fari a jiya litinin, jam'iyyar SPLM ta ce a shirye ta ke ta shiga zaben jam'iyyu da dama na farko da kasar zata gudanar tun shekarar 1986.

A lokacin da ta ke magana da 'yan jarida a birnin Juba, mataimakiyar sakatare-janar ta jam'iyyar SPLM., Anna Itto, ta ce jam'iyyarsu ba ta taba goyon bayan kiraye-kirayen jam'iyyun hamayya na arewacin kasar cewar a jinkirta zaben da ake shirin gudanarwa a watan Afrilu ba.

Zaben wani muhimmin bangare ne na yarjejeniyar zaman lafiya ta 2005 wadda ta kawo karshen yakin basasar arewaci da kudancin Sudan.

XS
SM
MD
LG