Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Tana Kira A Kafa Dokoki Da Zasu Tinkari Taaddanci


Rasha Tana Kira A Kafa Dokoki Da Zasu Tinkari Taaddanci

<!-- IMAGE -->

Shugaba Dmitiri Medvedev na kasar Rasha yayi kira da a fito da sabbabin dokokin da zasu tinkari akidar ta’addanci. Yana maganar ne kuwa a daidai lokacinda al’ummar Rasha din ke cikin makokin juyayin asaran rayukka 39 da suka hallaka jiya Litinin a cikin bama-baman da suka tashi akan jiragen karkashin kasa na birnin Moscow.

Jawabin telebijin din da shugaban Rashar yayi, yazo ne a lokacinda mutane ke zuwa suna ajiye furrani da kunna kyandir da ajiye hotunan wasu daga cikin mutanen da suka mutun a bakin biyu daga cikin tashoshin jiragen da aka auna a harin na jiya.

Koda yake har yanzu ba wata kungiyar da ta fito ta dauki alhakin kai harin, hukumomin Rashar sunce wasu ‘yan kunar bakin wake biyu mata dake da alaka da wasu kungiyoyin kishin Islama na yankunan kudancin rasha ne suka kai farmakin.

XS
SM
MD
LG