Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi Ya Rasu


Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi Ya Rasu

<!-- IMAGE -->

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, ya rasu cikin daren lahadi, a bayan da 'yan fashi suka tare su suka yi musu fashi dab da kauyen Darki, kusa da garin Takai a kan hanyarsu ta komawa Kano daga Jihar Bauchi.

Wakilin Muryar Amurka a Kano, Muhammadu Salisu Rabi'u, ya bada rahoton cewa marigayi Abubakar Rimi, bai ji rauni lokacin fashin ba, amma ya isa gida yana fama da ciwon kirji. An ce daga nan aka garzaya da shi zuwa asibitin Mallam Aminu Kano, inda ya cika a cikin daren.

Zuwa jimawa yau da hantsin litinin za a yi jana'izarsa a Kano.

An haifi marigayi Abubakar Rimi a shekarar 1940 a kauyen Rimi dake yankin Karamar Hukumar Sumaila a Jihar Kano.

Ya zamo gwamnan Jihar Kano a shekarar 1979 lokacin da aka maida mulki hannun farar hula a Jamhuriya ta biyu. Yana cikin jigogin da suka kafa Jam'iyyar PDP wadda ta ke mulkin Nijeriya a yanzu haka.

XS
SM
MD
LG