Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da samun taimakon gaggawa don citon ral.


Da samun taimakon gaggawa don citon ral.

<!-- IMAGE -->

Ko da mace bata da wata lalura, yana da kyau tare da fa'ida, ta nufi babban asibiti idan nakuda ta kankama don samun haihuwa lafiya cikin sauki. Idan mai nakuda tana asibiti, duk wata lalurar data taso kafin mace ta jigata, zata samun taimakon gaggawa wajan haihuwa, ta hanyar yi mata allurar nakuda, in kuma yaro yazo a gicciye, wannan sai likita yayi fida, a fitar da jariri don a ceci rayuwar mace da jaririn dake cikin mahifa, in kuwa a gida ne, tabbas sai dai tayi ta shure-shure har wa'adi ya cika ta mutu.

Doguwar nakuda shine babban lamarin dake haddasa kamuwa da ciwon yoyon fitsari in ba a je asibiti ba. Kamar a gida unguwar zoma ta gargajiya tana yin yankar gishiri ko yankar gurya. A asibiti, kwararrun likitan fida ne zai yi aikin cikin sauri da natsuwa a dinke wurin don hana shigar ciwon yoyon fitsari

Saboda haka, ya ku yan'uwa magidanta da dangin amarya da maji, mu rungumi akidar zuwa babban asibiti idan haihuwa tazo ga iyalanmu.

Wani babban lamari kuma, shine samun allurer rigakafi na farko da ake yiwa mai jego da jariri jin-kadan da an tsaftace yaro bayan haihuwa. Wacce duk ba a asibiti ta haihu ba, kenan tayi hasarar wannan rigakafin, kuma rashin shi yake haddasa mutuwar mai jego ko kuma jaririn data haifa kafin ranar suna ko cika kwana arba'in da haihuwa.

Muryar Amurka VOA Hausa tana shawartan magidanta da su hamzarta kai mai jego da jaririnta zuwa asibiti cikin gaggawa wato mintoci bayan an haihu domin wasu Allah yana basu ikon haihuwa cikin sauki a gida.

XS
SM
MD
LG