Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan


<!-- IMAGE -->

Mai rikon mukamin shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya gana jiya lahadi da shugaba Barack Obama na Amurka a Washington.

An yi wannan ganawa a ziyarar farko da Mr. Jonathan ya kai wata kasar waje tun watan Fabrairu, a lokacin da ya karbi ikon gudanar da mulkin kasa daga hannun shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa mai fama da rashin lafiya.

Shugabannin na Najeriya da Amurka sun yarda zasu yi aiki tare kan batutuwan tsaro a duniya, da hana bazuwar makaman nukiliya da kuma yaki da ta’addanci.

A lokacin wannan ganawar, Mr. Obama ya jaddada muhimmancin da Amurka ta dora a kan dangantakarta da Najeriya. Mr. Obama ya ce muradin Amurka ne ta ga Najeriya ta zama kasa mai karfi, mai bin tafarkin dimokuradiyya kuma mai arziki.

Mr. Jonathan yana daya daga cikin shugabannin kasashe kusan 50 wadanda Mr. Obama ya gayyata domin halartar taron kolin kwanaki biyu kan hana yaduwar makaman nukiliya.

A makon jiya, Amurka da Najeriya sun kafa wata Hukumar Tuntubar Juna ta Hadin Guiwa wadda zata taimakawa Najeriya wajen kyautata yadda ake mulkin kasar da kuma yaki da cin hanci da zarmiya.

XS
SM
MD
LG