Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Mutu A Girgizar Kasa Ya Karu A Kasar Sin


Adadin Wadanda Suka Mutu A Girgizar Kasa Ya Karu A Kasar Sin

<!-- IMAGE -->

Kafofin labarai na gwamnatin kasar Sin sun ce yawan mutanen da suka mutu a girgizar kasa mai karfi a yammacin kasar ya karu zuwa 617. Mutane fiye da dubu 10 sun ji rauni, wasu fiye da 300 ba a san inda suke ba a bayan wannan girgzia mai karfin kusan awu 7 wadda a jiya laraba ta rushe gine-gine, ta lalata hanyoyi, ta tsinke wayoyin tarho da na wutar lantarki a lardin Qinghai mai iyaka da Tibet.

Kasa ta ci gaba da motsi a bayan babbar girgiza ta farko. Idanun babbar girgizar ta farko yana gundumar Yushu ta ‘yan jinsin Tibet a kudancin lardin Qinghai.

Masu aikin agaji su na kokarin tono mutanen dake karkashin gine-ginen da suka rushe. An tura ma’aikata dubu 5 cikinsu har da sojoji da likitoci da masu aikin ceto zuwa yankin.

Shugaba Hu Jintao da firimiya Wen Jiabao sun umurci hukumomin yankin da su dauki dukkan matakan da zasu iya domin ceto mutanen da abin ya shafa. Nan take gwamnatin kasar Sin ta ware dala miliyan 29 don tallafawa ayyukan agaji ciki har da kwashe mutane da sake tsugunarwa da kuma jinya.

A yayin da wasu karin mutane ke rasa matsuguni su na fitowa waje cikin sanyin hunturu na yankin, gwamnatin lardin Qinghai ta ce zata garzaya da tantuna dubu 5 da rigunan sanyi da barguna dubu 100 zuwa yankin.

XS
SM
MD
LG