Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsayin Shugaba Bush a gameda Afghanistan - 2001-08-29


Shugaba Bush, ya soma hutun karshen mako na bukin cika-ciki wajen shiryawa tareda nazarin taron kasa da kasa da za’a gudanar a makon gobe domin shata makomar Afghanistan. Ranar Juma’a Shugaba Bush yayi jagorancin wani taro da aka shirya ta hanyar hada hancin jami’ansa na tsaron kasa daban daban ta fasahar na’urar magana kai tsaye cikin akwatin telebijin. Ya zanta da jami’an nasa daga dandalin shakatawar shugabannin Amirka na Campo David. Taron da ake shiryawa tareda wakilan siyasa daban daban na Afgahnistan za’a soma ne daga Talata mai zuwa, 27 ga watan Nuwamba a birnin Bonn na Jamus. A farkon wannan mako Mr Bush ya gayawa mayakan Amirka cewa yana neman tabbatarda ganin Afghanistan ta samu gwamnati mai wakilcin dukkan sassan al’ummar kasar.

XS
SM
MD
LG