Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martani kan Kashe Bola Ige - 2001-12-27


To daya daga cikin mutanen da suka fi kusa da marigayi Bola Ige, musamman ma a bangaren ’yan siyasar Yarbawa masu akidar Awolowo, shine tsohon ministan harkokin wajen Nijeriya farfesa Bolaji Akinyemi. Sunday Dare ya tambayi Farfesa Akinyemi, ko me yake gani wannan kisa na Bola Ige zai iya haifarwa, sai ya ce...

ACT: AKINYEMI: “Normally, the death of one man diminishes all of us, but the political assassination of the......”

VOICE: A mafi yawan lokuta dai, mutuwar mutum guda, ta kan zamo hasara ga dukkan jama’a, amma yin kisan gilla wa atoni janar na Nijeriya kuma ministan shari’a, wannan tamkar girgizar kasa ce a fagen siyasa. Wannan abu ne mai girgizarwa, wanda ya buwayi tunani. Ba mu taba ganin kisa na siyasa a irin wannan matsayi ba. Wannan abu yana da matukar muni. Nayi imani da cewa mun yi sakaci mun kyale tarzoma ta shiga cikin harkokinmu na siyasa, kuma wannan sakamako ne na wannan lamarin. Babu wata hujja da mutum zai iya gabatarwa ta yin irin wannan kisa. Bola Ige mutum ne mai tunani da basirar lafazi, gogaggen dan siyasa wanda ayyukansa cikin shekaru 40 da suka shige sun shafi kowane bangare na wannan kasa. Ina fata dukkan ’yan Nijeriya, da dukkan ’yan siyasarmu, zasu ajiye bambancin siyasa da na harshe ko kabilanci a gefe guda, su hada kai, su fito da babbar murya kuma da kuzari, su yaki wannan cuta mai muni ta tarzoma wadda ta shigo cikin harkokin siyasarmu. Daga nan Sunday Dare ya tambayi Bolaji Akinyemi ko ta yaya wannan kisa na Bola Ige zai shafi al’ummar Yarbawa musamman, da kuma yankin kudu maso yammacin Nijeriya da kokarin kafa dimokuradiyya a Nijeriya, sai ya ce...

ACT: AKINYEMI: “Well, I don’t think really any purpose is served by particularizing it in terms of the Yoruba race...”

VOICE: Ina jin cewa babu wani alfanu na bayyana wannan a zaman hasara ga al’ummar Yarbawa kawai. A cikin shekaru biyu da rabin da suka shige mun yi ta ganin kashe kashen siyasa a kasar nan, koda yake duk cikinsu babu wanda ya girgiza jama’a ko zai iya dora tassiri kamar kisan Bola Ige. A saboda haka zamu kaskantar da kisan Bola Ige ne idan muka bayyana shi a zaman lamari ko matsala ta Yarbawa. Wannan matsala ce ta kasa baki daya, wadda ta zamo dole dukkan al’ummar Nijeriya su taru su takale ta. A saboda haka, sai Sunday dare ya tambaye shi ko wace shawara zai bai wa gwamnatin Obasanjo kan wannan, sai Farfesa Bolaji Akinyemi ya ce.....

ACT: AKINYEMI: “First of all, in order to avoid disruptive and negative speculation, I will urge a thorough, rapid and public police investigation.....”

VOICE: Da farko dai domin mu gujewa rade-radi da jita-jitar babu gaira babu dalili, ina yin kiran da nan take ba tare da wani bata lokaci ba, ’yan sanda su kaddamar da bincike gadan gadan, a bainar jama’a domin gano wadanda suka aikata wannan kisa da kuma dalilansu. Sannan a gaggauta bayyana sakamakon wannan bincike ga jama’a domin su san abubuwan dake gudana. Na biyu, ya zamo tilas a kirkiro da wani dandali inda dukkan ’yan siyasar Nijeriya zasu hadu su tattauna su ayyana tashin hankalin siyasa ko kisan siyasa a zaman daya daga cikin illolin da tilas mu murkushe shi mu kawar da shi. Ba kawai gwamnati ce ko wata jam’iyya zata kira wannan taro ba, hakki ne da ya rataya wuyar kowa. Wata tambayar da aka yi ma Farfesa Bolaji Akinyemi kuma, ita ce shin ta yaya wannan kisa zata shafi akidar siyasa ta Awolowo. Farfesa Akinyemi, ya ce lokaci bai yi ba na auna wannan, tun da a yanzu kowa yana jimamin wannan mutuwa ce. Maimakon haka, ya ce ya kamata kowa ya maida hankalinsa kan wannan kisa da kuma ta yadda idan har aka yi ma ministan shari’a haka, to lallai kasa tana da matsala babba dake bukatar magancewa cikin gaggawa.

BRIDGE:-----------------------instrumental------------

VOICE: To, duk da cewa marigayi Bola Ige ya zamo ministan shari’a a Nijeriya, ya ci gaba da rubuta sharhin nan da ya saba yi mako-mako a jaridar Nigerian Tribune, daya daga cikin tsoffin jaridun Nijeriya. Ta yaya wannan jarida ta dauki labarin kashe Bola Ige? Wannan ita ce tambayar da Sunday Dare yayi ma Segun Olatunji, editan jaridar ta Nigerian Tribune, wanda ya kada ya ce.....

ACT: OLATUNJI: “We were shocked by it because we were not expecting it. We knew that there were some political problems in Yorubaland, but......”

VOICE: Wannan labarin ya girgiza mu, saboda ya zo mana haka kwatsam. Mun san cewa akwai rigingimun siyasa sosai a kasar Yarbawa, amma ba mu taba tsammanin cewar abin zai yi muni ya kai ga kisan gilla na siyasa ba. Na gana da shi kimanin wata guda da ya shige a gidansa, inda yake bayyana mini yadda yake son ganin dimokuradiyya ta zauna da gindinta a wannan kasa tare da ganin cewa Yarbawa sun samu nasu rabon daidai gwargwado. Sharhin da yake rubuta mana yana da farin jini saboda kwarewarsa da lafazinsa da sanin luggar siyasarsa. To ta yaya ’yan jarida ke daukar wannan mutuwa ta Bola Ige, watau me ake gani a zaman musabbabinsa? Sai Mr segun Olatunji ya ce.....

ACT: OLATUNJI: “Some extension of the media think it might have arisen from the crisis between the governor of Osun state, Chief Adebisi Akande and his...”

VOICE: wasu ’yan jarida dai suna daukar cewa watakila wannan kisa yana da nasaba da rigimar siyasar da ake yi tsakanin gwamnan Jihar Osun, Cif Adebisi Akande da mataimakinsa, Cif Omishore. Musamman ma a bayan da aka kashe Mr Olagbaju, babban mai goyon bayan Cif Omishore kuma dan gaban goshinsa a majalisar dokokin jihar. Wasu kuwa suna jin cewa wannan kisan daga wani wuri ne dabam. Ya ce masu akidar siyasa irinta Awolowo sun yi babbar hasara, har ma iyalan marigayi Awolowo sun bada sanarwa suna bayyana jimamin mutuwarsa tare da bayyana cewa wannan babbar hasara ce a gare su.

XS
SM
MD
LG