Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Israel - Palestinians - 2002-01-04


Isra’ila ta ce ta kama wani jirgin ruwa cike da makamai da aka yi niyyar kaiwa zuwa yankunan mulkin kai na Falasdinawa. Rundunar sojojin Isra’ila ta ce sojojin kundumbala na ruwa sun shiga cikin wannan jirgi a tekun Bahar Maliya suka samu ton 50 na makamai, akasarinsu makamai kirar Iran, da rokoki samfurin Katyusha, da nakiyoyi tare da makamai masu linzami na ragargaza tankoki. Babban hafsan sojojin Isra’ila, Janar Shaul Mofaz, ya ce jirgin ruwan mallakar hukumar mulkin kai ta Falasdinawa ce, sannan kyaftin na wannan jirgi tare da ma’aikatansa ’yan sandan ruwa ne na Falasdinawa. Isra’ila ta bada sanarwar damke makaman ne a daidai lokacin da wakilin Amurka Anthony Zinni ya fara sabon yunkuri na kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin Bani Isra’ila da Falasdinawa. A lokacin, Mr Zinni yana tattaunawa da shugaban Falasdinawa Yasser Arafat a birnin Ramallah, bayan da ya gana da firayim ministan Isra’ila Ariel Sharon.

A yau Jumma’a da safe kuma, sojojin Isra’ila sun kai sumame wani kauyen dake yankin yammacin kogin Jordan suna farautar masu kishin Falasdinu. Sojojin na Isra’ila sun kashe mutum guda da aka ce yana dauke da makami suka kama wasu da dama a wannan kauye mai suna Tel kusa da Nablus. Hukumomin Falasdinawa sun ce mutumin da aka kashe dan sanda ne.

XS
SM
MD
LG