Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Girmama Muhammad Ali - 2002-01-11


Ranar talata takwas ga wannan wata Magajin Garin Los Angeles, jihar California, Jim Hahn ya tsayarda ranar tunawa da girmama gwarzon dambe bakar fata na Amirka. Magajin garin yana mai cewa ba shaharar tasa kadai ya sanya ya girmama shi ba, sai don halaiyarsa na agajin marasa galihu. Shi zakarar 'yan danben ya kasance a birnin a ranar da aka girmama shi. Haka wakilan majalisar birnin (ta karamar hukuma) sun baiyana irin yadda shi wannan sanannen dan dambe ya kuma zama gwarzon kare mutuncin bakar fata tareda nuna jarunta wajen kare dukkan abinda yayi imani da shi. Idan an tuna ya taba kin shiga aikin sojin Amirka yayin yakin Vietnam a saboda ya baiyana yakin a zaman wanda bai dace ba. 'Yar majalisa Janice Hahn, kanwar Magajin garin cewa ta yi ta tuna lokacinda Muhammad Ali ya taho duba mahaifinta a lokacinda baya da lafiya bayanda shan inna ta kama shi. A lokacinda ya ce ba zai sake tsayawa takara ba. Gwarzon damben ya karfafa masa cewa lallai ya tsaya, inda ya ce zai iya tura kekensa na guragu gida gida suna yankin neman zabe. Yayinda ake alfahari da wani majigin da aka yi a gameda rayuwarsa mai suna "Ali" a yau ne kuma za'a girmama shi ta hanyar sanya sunansa tsakanin gwarzayen wadanda suka yi fice a harkar wasanni a Hollywood.

XS
SM
MD
LG