Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aiki A Nijeriya - 2002-01-16


’Yan sandan Nigeria sun kama shugaban Babbar Kungiyar Kwadago, Adam Oshiomhole, a yayinda aka fara yajin aikin gama gari domin nuna rashin amincewa da karin kudin mai. An kama shugaban na kungiyar kwadago tare da wasu shugabanninta a lokacin wata zanga zanga a Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya.

’Yan sanda sunyi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa gungun mutane kimanin dari biyar magoya bayan shugabannin a yayinda suke kama su. Gidajen mai da wasu kantunan suna rufe.

A jiya talata gwamnati ta ayyana cewa yin yajin aikin, karya doka ce tana mai fadin cewa kungiyar kwadago ta keta ka'idojin doka domin bata bada sanarwar kwanaki ashirin da daya na shirin yin yajin aikin a rubuce kamar yadda doka ta tanada ba.

XS
SM
MD
LG