Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Waje Colin Powell Ya Isa Pakistan - 2002-01-16


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya isa kasar Pakistan, inda zai tattauna da shugaba Pervez Musharraf da sauran manyan jami‘an gwamnatin kasar kan batun gano hanyar rage zafin rikicin dake tsakanin India da Pakistan. Kafin ya tashi zuwa Pakistan, anji sakatare Powell yana cewa fatansa shine wannan ziyara tasa ta sami nasarar taimakawa wajen rage dimbin makaman yaki da sojojin da India ta jibge a kan iyakarta da Pakistan. Yace zai yi kira ga shugabannin kasashen biyu da su gaggauta shirya tattaunawa da juna domin a kai ga fahimtar juna don rage zargin juna game da rikicin yankin nan na Kashmir dake kan iyakokinsu.

Wani lokaci a wannan makon ne kuma Sakatare Powll zai ziyarci Indiya.

Anji Janar Musarraf na cewa Pakistan zata ci gaba da bada goyon bayanta ga kokarin da al‘ummar Kashmir dake bangaren Indiya keyi na neman ’yancin kansu.

XS
SM
MD
LG