Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Duniya Ya ce Za a Kashe Dala Miliyan Dubu 15 Don Sake Gina Afghanistan - 2002-01-16


Bankin Duniya yace za’a kashe dala miliyan dubu goma sha biyar cikin shekaru goma masu zuwa domin sake gina Afghanistan. A jiya talata shugaban bankin, James Wolfensohn, yayi wannan furuci bayan da bankin nasa da bankin raya kasashen Asiya da kuma Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya suka gabatar da rahoto akan yawan kudin da za’a kashe wajen sake gina wannan kasa da yaki ya daidaita. A halin da ake ciki, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya dage haramcin zirga zirgar daya azawa kamfanin jirgin saman kasar ta Afghanistan, ya kuma mika ma kamfanin kudi dala miliyan 23 na yin amfani da sararin samaniyar Afghanistan, wanda Kungiyar lura da zirga zirgar jiragen sama ta kasa da kasa ta hana a zamanin mulkin 'yan Taleban. Haka kuma ana sa ran a wannan mako Majalisar Dinkin Duniya zata kara daukar wasu matakai na kyale Afghanistan tayi amfani da ajiyar zinarenta na fiye da dala miliyan maitan da aka hanata amfani dasu.

A makon gobe idan Allah Ya kaimu ne kuma za’a fara taron kasashen da zasu, ko kuma suke, baiwa Afghanistan taimako a Tokyo kasar Japan.

XS
SM
MD
LG