Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba'Amurke Dan Taliban Zai Gurfana Gaban kotu - 2002-01-16


Atoni Janar na Amurka, John Ashcroft, yace za‘a gurfanar da Ba’amurken nan da aka kama tare da mayakan Taleban a kasar Afghanistan gaban kotun dake shari‘a farar hula domin amsa tuhumar da ake masa ta taimakawa ’yan ta’adda. A jiya Talata ne Mr. Ashcroft yake cewa ana tuhumar John Walker Lindh da laifin taimakawa kungiyar al-Qaida wajen shirya karkashe sojojin Amirka a kasar waje.

Idan kuwa kotun ta sameshi da laifi, yana iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai, amma ba hukuncin kisa ba.

Atoni Janar na Amirka yace shi da kansa Mr. Walker ne ya amince yayi bayanin abinda ya aikata ga jami‘an bincike, inda yace ya sadu da shugaban al-Qaida Osama bin Laden a wani sansanin horas da ’yan tadda, sannan ya amince da ya shiga sahun ’yan ta‘addar dake yaki da Amurkawa, bayan kuwa ya sani cewa ‘yan ta‘addar sun kashe dubun dubatar ’yan'uwansa Amurkawa a ran sha daya ga watan Satumban da ya gabata.

XS
SM
MD
LG