Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kundumbalar Amurka Biyu Sun Mutu a Afghanistan - 2002-01-20


Sojojin kundumbala biyu na Amurka sun mutu, wasu biyar kuma suka ji rauni a lokacin da jirgin samansu mai saukar ungulu ya fadi a wani yanki mai duwatsu na gabashin Afghanistan. Wani kakakin sojojin Amurka ya ce jirgin ya fadi a wani wuri mai tazarar kimanin kilomita 60 daga sansanin mayakan sama na Bagram. Ya ce jirgin yana daya daga cikin guda biyu da suka tashi daga sansanin domin aikin jigilar karin kayayyaki. Kakakin ya ce biyu daga cikin sojojin kundumbalar da suka ji rauni suna kwance rai hannun Allah, kuma an kwashe dukkansu biyar masu rauni.

Ana binciken musabbabin faduwar wannan jirgi.

Wani kakakin rundunar sojojin kundumbala ya ce babu wata alamar cewa abokan gabarsu ne suka harbo jirgin, amma kuma ba za a iya cewa ba hakan ne ya faru ba.

A halin da ake ciki, shugaban gwamnatin rikon kwarya a Afghanistan, Hamid Karzai, yana birnin Tokyo, domin halartar wani muhimmin taron kasashen duniya kan bada agaji ga kasarsa da yaki ya lalata. Idan aka kaddamar da wannan taron kwanaki biyu a ranar litinin, kasashe kusan 60 tare da kungiyoyi na kasa da kasa masu yawa zasu nazarci bada agajin dubban miliyoyin daloli.

Malam Karzai ya ce yana fatar komawa ga al’ummarsa dauke da kwarya a cike, ta yadda za a fara sake gina Afghanistan a bayan yakin shekara da shekaru. Ana sa ran cewa mai masaukin baki Japan da Amurka da Kungiyar tarayyar Turai da kuma Saudi Arabiya sune zasu bada gudumawar kudi mafi tsoka da ake bukata domin sake gina kasar. Hukumomi na kasa da kasa sun ce sabuwar gwamnatin Afghanistan zata bukaci agajin kudi dala miliyan dubu 5 cikin watanni 30 masu zuwa.

XS
SM
MD
LG